Jiya Lahadi shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ya “sake wani tunanin” game da ci gaba da ta'azzarar da harajin ramuwar gayya ke yi tsakanin Amurka da China, amma Fadar White House ta yi sauri ta yi karin haske da cewa ya na nufin da ma ya kara haraji ma China fiye da yadda ya yi.
WASHINGTON DC —
A makon da ya gabata, kafin ya tashi zuwa Faransa don halartar taron shugabanin kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki, Shugaba Trump ya kara harajin dala biliyan $550B akan kayayyakin China da ake shigar da su Amurka, bayan da Chinar ta ce za ta kara harajin dala biliyan $75B kan kayayyankin Amurka da ake shigar da su China, wanda shi ma martani ne na karin harajin da Trump ya yi mata gabanin nan.
A jiya Lahadi, yayin da ya zauna don yin taron karin kumollon safe tare da sabon Firaiministan Birtaniya, Boris Johnson, ‘yan jarida sun tambaye shi ko ya na da na sanin saka harajin ramuwar gayyar da su ke yi da China, sai ya ce, Trump ya amsa da cewa, "Eh, tabbas. Don me ba zan yi."'