Rikicin Ivory Coast Ya Sa Mutum Miliyan Daya Barin Gidajen Su

'Yan Gudun Hijirar kasar Ivory Coast su na jira a yi mu su rajista a wani sansanin Majalisar Dinkin Duniya a Laberiya

Hukumar kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Ta ce 'Yan Kasar Ivory Coast Miliyan Daya sun Arce Daga Gidajen Su Saboda Rikicin Bayan Zabe.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce a kasar Ivory Coast mutanen da yawan su ya kai miliyan daya sun tsere daga gidajen su saboda rikicin da ya biyo bayan zabe.

Mai magana da yawun hukumar, Melissa Fleming, ta gayawa manema labarai a yau Jumma'a cewa tsoron yakin da ake yi gadan-gadan ne ke yiwa tulin jama'a kaimin gudu daga gidajen su.

Masu gudun hijira daga kasar Ivory Coast zuwa kasar Laberiya.

Hukumar ta kiyasta cewa mutanen da yawan su ya kai Dubu Dari Bakwai zuwa Miliyan daya ne su ka gudu daga gidajen su, akasarin su daga birnin Abidjan, cibiyar hada-hadar kasuwancin kasar.

Birnin na Abidjan ya zama fagen daga tsakanin magoya bayan shugabannin kasar biyu masu jayayyar mulki da juna.

Mayakan sa kai a birnin Abidjan wanda ya zama fagen daga a 'yan kwanakin nan .

Wata hadakar kungiyoyi Talatin da Biyu, na kasa da kasa ta fada a yau Jumma'a cewa al'amarin tagayyarar bil Adaman da ke faruwa a kasar Ivory Coast ya kai wani matsayi mai tsanani.

Shugaba mai ci Laurent Gbagbo ya ki mika mulki ga Alassane Ouattara wanda kasa da kasa su ka amince cewa shi ne ya yi nasara a zaben shugaban kasar da aka yi a cikin watan Nuwamba.

Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya na shirin duba rikicin siyasar a yayin wani zaman taron da zai yi yau Jumma'a a birnin New York.

A jiya Alhamis wani gungun shugabannin kasashen yammacin Afirka ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta karfafa aikin tsaron zaman lafiyar da aka ba ta izinin yi a kasar Ivory Coast kuma ta kwakubawa Mr. Gbagbo takunkumin ladabtarwa.

Su ma kasashe Goma Sha Biyar na kungiyar ci gaban tattalin arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS/CEDEAO) sun yi kira ga ofishin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Ivory Coast da ya taimaka wajen mika mulki daga Mr.Gbagbo zuwa Mr.Ouattara.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce daga barkewar rikicin ya zuwa yanzu, an kashe mutane Dari Hudu da Sittin da Biyu (462) a kalla.