Rahotannin da ke fitowa daga kamfanin matatar man Dangote da ke Lekki na jihar Legas na cewa yanzu haka kimanin matocin dakon man fetur na kamfanin mai na kasa a Najeriya NNCPL 300 ne suka fara dakon man fetur domin sayar wa a gidajen man fetur a Najeriya.
Fara sayar da man a ranar Lahadin nan ya biyo bayan yarjejeniyar da aka kulla ne tsakanin kamfanin na Dangote da kuma kamfanin NNPCL.
Ricikin farashin man fetur ya barke tsakanin Kamfanin NNPCL da kamfanin Dangote bayan da NNPLC ya ce ya sayi kowace lita a kan Naira 898, farashin da kamfanin Dangote ya ce ba gaskiya ba ne.
A wata sanarwa da kamfanin Dangote ya fitar ya ce ya sayarwar da kamfanin NNPCL da man fetur din da kudin dalar Amurka ba da Naira ba.
Wannan ya nuna cewa farashin man a gidajen mai ba zai gaza Naira 900 ba ke nan, ko da kuwa a birnin Legas ne mai abin hawa zai sayi man.
Da yake tsokacin kan ko ta yaya samar da man a cikin gida zai taimakawa tattalin arzikin Najeriya, Dakta Dauda Mohammed Kontagora, masanin tattalin arziki ne da saka jari a Najeriya, ya ce wannan abin yabawa ne, sai dai babu sauki ga ‘yan kasa, tun da NNPCL ta gaje kasuwar a yanzu.
Kamfanin NNPCL, wanda ke da matatun man fetur 4 da Depot-Depot a jihohin kasar da dama, ya kasa sarrafawa da rarraba man fetur a cikin shekaru fiye da 25.
Kamfanin NNPCL yana sayo man da yake sayarwa daga danyen mai a kasashen waje, abin da kuma ke haifar da asara da tsadar mai a cikin gida.
Sai dai yanzu haka kamfanin man na Dangote ya musanta bayanan da NNPCL ya fitar da ke cewa ta sayi man ne a kan kudi Naira 898 a kan kowace lita.
Kamfanin Dangote duk da cewar bai fadi farashin da ya sayar wa da NNPCL ba, ya ce ya sayar masa ne da kudin dalar Amurka kuma kasa da yadda NNPCL ta saba sayowa a kasashen waje.
Saurari cikakken rahoton Babangida Jibrin:
Your browser doesn’t support HTML5