Rikicin Da Ya Kunno Kai A Majalisar Wakilan Najeriya

ABUJA: KAKAKIN MAJALISAR WAKILAI DA MATASA

Bayan tsohon Shugaban Komitin Kula da Kasafin Kudi a Majalisar Wakilan Najeriya Abdulmumuni Jibrin ya fasa kwai mai wari, inda ya zargi Shugabanin da yin abin da ya kira mummunan aringizo a kasafin kudin bana, mai Magana da yawun Majalisar Abdurazak Namdas ya fito ya kare shugabanin.

Tun ranar 20 ga wannan wata ne dai tsohon kwamitin kasafin kudi a Majalisar Wakilan Najeriya, Abudulmumuni Jibrin, yayi zargin cewa manyan shugabannin Majalisar ciki harda kakaki Yakubu Dogara da mataimakinsa Sulaiman Lasu da mai tsawatarwa Alhassan Ado Doguwa da kuma shugaban marasa rinjaye Leo Ogor, sunyi aringizo a kasafin kudin bana har na Naira Biliyan 40.

Mai magana da yawun Majalisar Abdurazak Namdas, ya bayyana a matsayin kuskure inda yace maganar kasafin kudin shugaban kasa ne ya amince yasa hannu ya amince da cewa ga kudi kuje kuyi aiki. Kuma Majalisa ta amince, cikin maganar babu wani laifi da aka aika kan wannan kasafi.

Kungiyar Transparency Group a majalisar wakilan, karkashin jagorancin Mohammed Musa Soba, sunyi tsokaci akan rikicin da ya kunno kai a Majalisar, da yin kira ga kakakin Majalisar da ya gaggauta maido da ‘yan Majalisar daga hutu domin su wanke kawunansu daga wannan zargi.

Saurari cikakken rahotan Madina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Rikicin Da Ya Kunno Kai A Majalisar Wakilan Najeriya - 3'20"