Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Komawar Nuhu Ribadu APC Ta Sa Jam'iyyar Ta Dare Biyu A Jihar Adamawa


Nuhu Ribadu yayinda ake sake yi masa rajistar shiga APC
Nuhu Ribadu yayinda ake sake yi masa rajistar shiga APC

Yau dai fiye da makwanni biyu ke nan ake fama da wannan rikici na jam’iyar APC a jihar Adamawa inda ta kai aka samu bangaren yan mu aka samu,da kuma yan bangaren gwamnan jihar Sanata Muhammadu Bindo Umaru Jibrilla,dake tare da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

Wannan kuma ya biyo bayan umarnin da uwar jam’iyar ta kasa ta baiwa shugabanin jam’iyar a Adamawa ne na cewa su hanzarta karbar wasu tsoffin kusoshin jam’iyar irinsu Mallam Nuhu Ribadu,tsohon shugaban hukumar EFCC,batun da wasu kusoshin jam’iyar ke cewa ba zata sabu ba.

ADAMAWA: Nuhu Ribadu da wasu shugabannin APC
ADAMAWA: Nuhu Ribadu da wasu shugabannin APC

Hon.Ibrahim Hassan Bapetel wani hadimin shugaban Najeriya kan ayyuka da tsare tsare,yace ,ai jam’iyar ba gadon wani ba ce,da za’a hana wasu komowa. Kana yace,jam’iyar APC ,jam’iyace ta kowa wadda kofar ta a bude take don masu son komowa.

Shima wani jigon jam’iyar Mr Kube Wiberforce Donbulom,kuma tsohon shugaban karamar hukumar Guyuk,yace,’’kamata yayi a yabawa tsoffin shugabanin da suka kawo jam’iyar a jihar irinsu tsohon gwamnan jihar Murtala Nyako,da kuma katukan Adamawa Mr Kobis Ari Thinmu.’’

Sakataren tsare tsare na jam’iyar a jihar Ahmad Lawal,yace su basu da wani bangare,inda yace wannan dambarwa bata rasa nasaba da irin hadakar da ta faru lokacin aka kafa jam’iyar a Najeriya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG