A taron manema labarai da Onarebul Abdulrazak Namdas ya kira ya musanta zargin da tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar ya yi akan kakakin majalisar.
Namdas ya bayyanawa Muryar Amurka abubuwan da ya fada. Yace duk wani zargi da Onarebul Abdulmummuni Jibrin ya yi akan kakakin majalisar da sauran shugabannin majalisar ba gaskiya ba ne. Yace duk abun da ya fada ba gaskiya ba ne.
Yace abun da shugaban kasa yake da niyar kashewa shi zai mikawa majalisa. Sai bayan majalisa ta zauna kai ta tantance, ta kara ko ta rage kasafin kuma shugaba ya sa hannu ya zama kasafin kudi a hukumance.
Yace lokacin da shi Abdulmummuni Jibrin ya yi shugabancin kwamitin kasafin kudi sun samu korafe korafe da yawa dalili ke nan da suka cireshi. Shi ne, wai, a lokacinsa baya aiki da sauran 'yan kwamitin sai ya boye yayi abun da ransa yake so.
Onarebul Namdas yace babu dan majalisa daya da ya fito yace abubuwan da Jibrin ke fada akwai gaskiya ciki. Yace zasu kai maganar gaban kwamitin majalisar a binciki abubuwan da yake fada domina san gaskiya.
Ga karin bayani.