Rikicin Benue: Buhari Ya Nuna Bacin Ransa Ga Shugaban 'Yan sandan Najeriya

Buhari Tare Da Gwamnan Benue

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kai ziyara jihar Benue domin jajintawa da kuma kiran jama’a su a zauna lafiya, saboda rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya da jihar ke fama da su.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa ya nuna bacin ransa sosai ga Sifeta Janar na 'yan sandan kasar, Ibrahim Idris, saboda kisan da aka yi a jihar Benue.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin ziyarar jaje da ya kai wa al'umar jihar ta Benue wacce take fama da rikicin makiyaya da manoma kamar yadda jaridun Najeriya suka wallafa a shafukansu na yanar gizo.

A cewar jaridar Daily Trust, wacce ta ruwaito kalaman Femi Adesina da ke bai wa shugaba Buhari shawara kan harkokin yada labarai, Buharin ya ce ba ya son yi wa mutane fada a baina jama'a, ya fi so ya ja mutum gefe ya nuna mai fushinsa.

Tarzoma tsakanin makiyaya da manoma, ta haddasa asarar rayuka da dumbin dukiyoyi da dama a jihar.

Shugaba Buhari, wanda ya isa Birnin Makurdi da misalin karfe 11 na safe ya kuma yi kira ga al’umar jihar da su zauna lafiya.

Ya kuma gana da gwamnan jihar ta Benue, Samuel Ortom, inda ya nemi masu ruwa da tsaki da suka hada da ‘yan siyasa da sarakunan gargajiya, su ba da gudunmuwarsu wajen tabbatar da zaman lafiya.

Sannan shugaban ya yi bayani kan irin matakan da gwamnatinsa ke dauka domin ganin an dakile wannan matsala.

Saurari rahoton tattaunawar wakiliyar Muryar Amurka, Zainab Babaji da Ibrahim Ka’almasi Garba:

Your browser doesn’t support HTML5

Rikicin Benue: Buhari Ya Nuna Bacin Ransa Ga Shugaban 'Yan sandan Najeriya 2'30"