Rikici a Harkokin Cinikkayya Da Siyasa Na Barazana Ga Tattalin Arzikin Duniya - Ministocin G20

G20 Argentina

A ranar Lahadi ministocin suka yi wannan furuci bayan taron kwanaki biyu da suka yi a birnin Buenos Aires na kasar Argentina.

A sanarwar bayan taron da suka gabatar,Ministocin sun jadadda bukatar dake akwai na karfafa yin shawarwari da daukan matakan magance wannan barazana da kara karfafa guiwa.

Ministocin da suke wakiltar kasashe masu arzikin masana’antu da masu tasowa, sun baiyana cewa tattalin arzikin duniya yana bunkasa, to amma sun baiyana damuwa akan abinda suka kira kasada ko kuma barazana na gajere da matsaikacin lokaci.

Basu ambaci Amurka a sanarwar bayan taro ba, amma wasu daga cikin su, basu ji dadin matsayin shugaban Amurka Donald Trump akan kudin fito daya karawa kayayyakin da China da kuma turai suke sayarwa Amurka ba.