Rikice-rikice na cikin jam'iya mai mulki a Najeriya sun fara bulla ne tun lokacin da aka gudanar da zabubukan shugabanni a matakin mazabu to sai dai wadanda ke ganin anyi masu ba daidai ba sun hakura har aka kai ga zabubukan kananan hukumomi.
Zabubukan shugabanni a matakin Jihohi shi ne ya kara fitowa da dambarwar a fili inda har aka gudanar da zabubukan daban-daban na makamai daya a wasu Jihohi inda yanzu haka rikice-rikicen na wanzuwa a wasu Jihohi duk da shawagin da kwamitin sasanta ‘ya'yan jam'iyar na kasa ke yi a wadannan Jihohin.
Jihar kebbi dake Arewa maso Yammacin kasar na daga cikin Jihohin da rikicin ya shiga tsakanin jam'iyar gida biyu.
Masu biyayya ga bangaren tsohon gwamna Adamu Aliero sune suke korafin ana yi masu bita-da-akulli inda yanzu haka wasu daga cikin wadanda aka tube daga makaman su suna kotu, sauran ‘yan jam'iyar sun ce babu hannun shugabannin da aka tube ga bude sabon ofishi.
Da muka zanta da Isa Assalafi wanda shine kakakin jam'iyar ya ce rabuwar ta yi wa al’umma dadi domin za ta basu damar su zabi, zabin su kuma su a matsayin shugabannin dimokradiyya na kasa suna murnar jama’a za su amfana kuma su fahimci abinda ke wakana.
Masana lamurran dimokradiya na ganin cewa yin karan-tsaye da manyan siyasa ke yi ga jam'iyun siyasa shine ke haifar da ce-ce-ku-ce wanda kuma kan iya tarwatsa su kuma su kasance marasa tasiri a kasa.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5