'Yan Majalisar Dokokin Najeriya sun yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu, wakar mubaya'a bayan da ya mika kundin kasafin kudin shekara ta 2024 a gaban Majalisar. Wannan dai shine karo na farko da aka taba yin haka a Majalisar.
Sanata mai wakiltan jihar Nasarawa ta yamma Ahmed Aliyu Wadada, na cikin wadanda suka kalli al'amarin ta wata fuska, inda ya ce wannan abu ne na bakin ciki da ke nuna kaskanci, kasancewar babu wani take da za'a yi a Majalisar kasa ban da taken Najeriya.
Wadada ya ce duk da cewa jamiyyar sa daya da ta shugaban kasa ba, amma ya ba shi izini idan ya ga wani abu wanda bai yi daidai ba, ya tuntube shi, saboda haka shi zai gaya wa shugaban kasa ba'a yi daidai ba a wannan wuri.
Shi ma kwararre a fanin zamantakewar dan Adam kuma malami a jami'ar Abuja, Dakta Farouk Bibi Farouk, ya ce wannan abin mamaki ne da al'ajabi har da tsoratarwa, amma za'a iya ta'allaka shi da cewa yawancin ‘yan majalisar sababbi ne kuma ba su san ka’idojin majalisar ba.
Amma ga masanin shari'a da kundin tsarin mulkin kasa Barista Mainasara Umar, na ganin kamata ya yi majalisa ta bi doka wajen gudanar da komi na ta.
Mainasara ya ce alamu ne na rashin nagarta na masu mulki, saboda su ne ke da hakkin tsaftace ayukan bangaren zartarwa, amma kuma sun nuna rashin da'a a wannan lokaci da suka rera waka a zauren majalisa.
A bin jira a gani shine matakin da shugabanin kasa da na Majalisar Dokokin za su dauka nan gaba, bayan tuntubar wasu 'yan kasar da suka ce za su yi kan wannan batun.
Domin karin bayani saurari rahotan Medina Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5