Da ribar sana’ar da nake yi a yanzu na shiga jami’a inda nake karantar kwas din Islamic studies a jamiar Bayero ta Kano duk ta hanyar alfanun sana’ar hannu domin dogaro da kai, inji matashiya Ruqayya Adam Gwammaja.
Ta ce tun tasowarta ta fara sana’a tun lokacin tana makarantar sakandare a matakin karatu na biyu take kokarin sayar da kayan tande tande a makaranta, wanda shi yayi sanadiyyar jan hankalinta domin ci gaba da gudanar da harkokin kasuwanci.
Ku Duba Wannan Ma Farar Mace Ko Mayya Ce - Ra'ayin Wasu SamariMatashiyar ta kara da cewa ta jajirce tana gunadar da sana’oi da dama kuma kowacce sana’a da kakarta, ma’ana akwai lokacin da take sayar da kaya idan ta lura da yanayin da ake ciki.
Ruqayya ta ce babban abinda ke ci mata tuwo a kwarya shine sha’ani bashi, da dama masu saye da zarar sun saya sai su fara wasan buya har wasu lokutan sai an dangana da hukuma kafin a kwato wa mai sana’a hakkin sa.
Daga karshe ta shawarci mata da su maida hankali wajen sana’oin dogaro da kai, domin a cewarta a yanzu rayuwa ta canza rayuwar aure ta zama wani yanayi na cudani in cude ka.
Your browser doesn’t support HTML5