Babban abinda ya kamata a ce matasa sun maida hankalin akai shine, samun ilimin zamani ba ya hana mutum cimma wani buri a rayuwa. Da yawa matasa na ganin cewar idan ka yi ilimin zamani, dole sai ka yi aikin gwamnati ko na kamfani.
Wannan shine dalilan da wasu kan yi amfani da su da cewar babu bukatar yin ilimin zamani. Amma a yanzu yadda duniya ke sauyawa, babu wani abu da mutum zai yi a rayuwa idan ba shi da ilimin zamani, domin kasuwancin zamani kullum daukar sabon salo ya ke yi.
Matashi Aliyu Mohammed Bello, yana ganin cewar lokaci ya yi da matasa za su mayar da hankali musamman wajen neman ilimin kimiyya da fasaha, wanda suke tashe a kasuwanin duniyar aiki. Domin kuwa duk wani fannin rayuwa a yanzu yana mayar da hankali akan yadda za'a inganta shi ta fannin kimiyya da fasaha.
Ku biyo mu don sauraron karashen wannan tattaunawa da daya daga cikin matasan Najeriya mafi kankantar shekarun da ba su wuce talatin ba, amma yana karatun digiri na uku wato Ph.D a kasar Birtaniya.
Facebook Forum