Ganin yadda ake barin mata a baya a harkokin siyasa na daga cikin dalilan da suka sa na ajiye aiki na, ba dan komai ba sai dan in kwatar wa mata ‘yancin su, da wayar masu da kai akan cikakken ‘yancin mata musamman a fagen siyasa.
Malama Na’ima, ta bayyana cewa bisa la’akari da yadda ake yiwa yawancin mata romon baka da basu abin da bai taka kara ya karya ba domin sauya masu ra’ayi akan wanda zai wakilce su, babban kalubale ne da ke bukatar a magance shi.
Kammar yadda aka san alfanun karatun ‘ya mace da tasirin sa a kowace al’umma, Malama Na’ima ta yi karatu a fannin kiwon lafiya, amma hakan bai sa ta manta da sauran mata ‘yan uwanta ba, a cewar ta, ganin yadda ake barin mata a baya wajan harkokin tafiyar da kasa na daga cikin dalilan da suka sa ta jajirce domin ganin an sami sauyi.
Daga karshe ta yi kira ga daukacin mata cewar kada su manta fa “duniya a hannu ta ke, dole sai mace ta tashi tsaye sa’annan ta sami ci gaba a rayuwa, kuma iyaye su kama mutuncin su tare da sa ‘ya’ya mata makarata domin tafiya da zamani.
Facebook Forum