ABUJA, NIGERIA - Kungiyar ta AMNESTY, ta kuma ce rayuwar talakawa za ta iya tsayawa cak matukar gwamnati ba ta cika alkawarin samar da hanyoyin sauki ba ga ‘yan kasa.
Tuni dai kayan masarufi su ka yi tashin gwauron zabi musamman don yadda sufuri ke shafar rayuwar tattalin arzkin kasa.
Daraktan kungiyar na AMNESTY a Najeriya Isa Sunusi ya ce sun lura duk muhimman sassan rayuwar 'yan Najeriya na da alaka da man fetur.
Talakawa sun so fakewa da kungiyar kwadago don mara baya ga yajin aiki ko matsawa gwamnati lamba ta sake matsaya amma zuwan 'yan kwadagon fadar Aso Rock ya sa su jingine matakai masu tsauri zuwa doguwar tattaunawa.
Za a jira a ga cika alkawarin shugaba Tinubu da ke cewa za a tura kudin tallafin zuwa wasi bangarori mafi amfani ga kasa.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5