Rawar Batsa Ta Janyo wa ‘Yan Mata ‘Dauri

Gulnara Karimova/RUSSIA FASHION WEEK

Wata kotu a gudancin kasar Rasha ta yanke wa wasu ‘yan mata uku hukuncin tsari na ‘dan wani lokaci a gidan yari, bisa laifin hada hotan bidiyo na rawar batsa da suka yi a kusa da ginin tarihi na yakin duniya na biyu.

Kasar Rasha dai zata yi bukin murnar cika shekaru 70 da samun nasarar yakin duniya na biyu a wata mai zuwa.

Wannan hukunci da aka yankewa ‘yan matan uku a kotun dake gundumar Novorossiyk, an yankewa ‘daya daga cikin matan mai shekara 19 hukuncin ‘daurin kwana 15 a gidan yari, sauran matan biyu masu shekaru ashirin ‘daurin kwana 10, lauya mai gabatar da shari’a ne ya nuna hotan bidiyon ‘yan matan suna rawar batsa ta zamani wadda suke yi suna juya ‘kugu kusa da ginin tarihin tunawa da yakin duniya na biyu.

Lauya mai gabatar da ‘kara ya fada a wani bayani da ya fitar cewa, ‘yan matan biyar dake cikin hotan bidiyon an same su da laifin nuna rashin ‘da’a, an kuma ‘daukewa ‘yan mata biyu daga ciki ‘dauri a dalilin rashin cikakkiyar lafiya.

Ire-iren laifuka na nuna rashin ‘da’a a kasar Rasha, laifine da kan kai mutum gidan yari an kuma yankewa mutane hukuncin ‘dauri ba sau ‘daya ba sau biyu ba, bisa aikata laifukan da suka danganci rashin kunya da ‘da’a.