A zantawarsu da wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma, malamin Jami’ar Cheick Anta Diop ta kasar Senegal Farfesa Boube Na Mewa, ya bayyana cewar rasuwar Mugabe babban rashi ne ga nahiyar Afirka.
Ya kuma kara bayani kan yadda Mugabe ya dauki aradu da ka a yunkurin taimakawa mutanen kasar Zimbabwe. Ya kuma mamaye dukan madafun ikon kasar tunda kasar ta sami 'yancin kai, sabilii da haka, banda gwamnatin mulkin mallaka, galibin al'ummar kasar basu san wani ba sai shi.
Koda yake wadansu suna yaba irin namizin kokarin da Mugabe ya yi wajen kare diyaucin kasar, da dama suna kushewa matakai da ya dauka da suka gurguntar da tattalin arzikin kasar suka kuma jefa al'ummar kasar cikin halin kunci.A wani bangare kuma an zargi Mugabe da mulkin kama karyar da keta hakin bil'adama da kuma kuntatawa abokan hamayya..
Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5