Shin Rasuwar Mahaifiyar Hama Amadou Zai Sa Ya Dawo Gida?

Jagoran 'Yan Adawa Hama Amadou.

A jiya Alhamis ne aka gudanar da jana’izar mahaifiyar jagoran ‘Yan Adawa a Jamhuriyar Nijer, Hama Amadou wacce Allah ya yiwa rasuwa a birnin Yamai.

Mambobin gwamnati da dama ne suka halarci taron bizne marigayiyar lamarin da ake ganin zai iya baiwa Hama Amadou kwarin guiwar dawowa gida daga gudun hijirar da ya shafe shekaru ya na yi a kasashen waje.

Zaman makokin kwanaki 10 ne uwar jam’iyar Moden Lumana Afirka ta fara a jiya alhamis domin nuna juyayin rasuwar mahaifiyar shuagaban babbar jam’iyar ta Adawa Hama Amadou.

Wasu jiga jigan gwamnatin PNDS Tarayya da kawayenta a karkashin jagorancin Ministan Cikin Gida Bazoum Mohamed sun halrci jana’izar mahaifiyar ta Hama Amadou abinda ke nunin siyasa ba gaba ba ce, inji kakakin jam’iyar ta PNDS Assoumana Mahamadou.

wasu ‘yan kasa na ganin wannan dama ce da jagoran ‘Yan Adawa ya kamata yayi amfani da ita don kawo karshen gudun hijirar da ya shafe shekaru ya na yi a waje, domin rashin halartar wannan zaman makoki na iya rage masa kwarjini a siyasance, sai dai makusanta na da tunanin da ya bambanta da wannan.

Abin tambaya a nan shine, "Shin Rasuwar Mahaifiyar Hama Amadou Zai Sa Ya Dawo Gida"?

Ga dai cikakken rahoto daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Rasuwar Mahaifiyar Hama Amadou Ya Sa Wasu Tambaya Ko Zai Dawo Gida