Daruruwan mutane ne suka yi gudun hijira daga garuruwa daban-daban saboda yawan hare-hare da sace-sacen mutane a wasu yankunan karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.
Al'ummar da suka fito daga garuruwa kusan 18, sun tare a wata makarantar firamare da ke garin Birnin Yero, Karamar Hukumar Igabi a jihar ta Kaduna domin neman mafaka.
Alhaji Jibrin Ya'u wanda shi ne Dagacin garin Jura, daya daga cikin garuruwan da 'yan gudun hijirar suka gudo, ya ce sace mutane da kuma karbar kudin fansa ya sa dole suka tsere daga garuruwan na su na haihuwa.
Sai dai wasu daga cikin wadannan 'yan gudun hijirar sun bayyana damuwa game da yadda gona ta gagara shiga musamman a yankin garin Jura da kewaye.
Su ma wasu mata sun ce bukatar su ita ce gwamnati ta kawo karshen barazanar tsaro ga mazajensu don su koma gida su ci gaba da noma.
A lokacin da yake ziyarar aiki a Litinin din nan saboda matsalar tsaron, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar kaduna, Samuel Aruwan, ya ce gwamnati na daukan matakan da suka dace.
Aruwan ya roki Al'umma da su rika taimakawa gwamnati da bayanan sirri don kawo karshen hare-hare da sace-sacen mutane a fadin jihar ta Kaduna.
Saurari cikakken rahoton wakilinmu Isah Lawal Ikara daga Kaduna:
Your browser doesn’t support HTML5