Saboda neman dalilin da ya sa tattalin arzikin Najeriya ya komade, Muryar Amurka ta zanta da Kasumu Garba Kurfi, wani masanin tattalin arziki wanda da yayi tsokaci akan dalilan da suka kai kasar ga wannan yanayi.
Kasumu Kurfi yace abun ya samo asali ne saboda yadda kasar ta cigaba da yin anfani da kudi lokacin da kudade ke shigowa ba tsagaitawa. Yace duk wanda aka ce yana samun kudi ko ta yaya ya kamata yayi tanadinsu domin gaba.
Shekaru biyar ko shida a baya kudade na shigowa kasar na fitar hankali amma kuma abun takaici, kasar bata yi tanadin da ya kamata ba, sai kasar ta dinga kashesu kamar gobe wasu zasu zo. Asalin inda aka fara samun matsala ke nan.
Abu na biyu da Malam Kurfi ya fada shi ne kasar bata koyon daratsi saboda lokacin Gowon da kudi suka shigo cewa yayi yadda kasar zata kashe ne matsalarta. Da kuma farashin mai ya fadi lokacin Shagari sai kasar ta shiga halin lahaula walakawati. Cikin wannan halin Buhari ya amshe mulki.
Da aka koma gwamnatin siyasa farashin mai bai daga ba amma kasar bata koyi daratsi ba. Da farashin mai ya sake hawa sama sai kasar ta koma gidan jiya ta cigaba da yin watanda da kudi. Ba'a tanadinsu kuma ba'a bi wata hanya ba a samowa kasar matsaya wadda ba tare da mai ba.
Idan kasa bata sarafa abubuwan da 'yan kasa ke anfani dasu a cikin gida, tattalin arziki na iya habaka na wani dan lokaci amma daga karshe zai durkushe.
Ga rahoron da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5