A wata ganawa da ya yi da Muryar Amurka, Barrister Jalo ya ce Mu’azu shi zai fi yin bayani bisa dalilin da ya sa ya yi murabus.
“Ni dai abin da na sani shi ne, ya ajiye aikin, ya ce ba zai iya ci gaba da mulki ba saboda ba shi da lafiya, amma bayanan da muke samu daga Adamu Maina Waziri da alama watakila ranar 29 ga watan Mayu lokacin da za a mika mulki akwai bayanan da Mu’azu zai yi.”
Da aka tambayeshi game da murabus din shugaban kwamitin dattawan jam’iyyar, Tony Anenih, Barrister Jalo ya ce watakila ya ajiye mukamin ne saboda nauyin cewa jam’iyyar ba ta yi nasara a karkashinsa ba.
“Ga dukkan alamu, Tony Anenih watakila ya ajiye mukamin domin ya ga cewa ya rike wannan mukamin kuma jam’iyya ba ta kai ga nasara ba, saboda haka ya ce bari ya baiwa wani wuri wanda watakila zai yi fiye da shi.”
Da aka tambayeshi shin babu walakin goro a miya gannin yadda manyan shugabannin jam’iyyar suka ajiye aikinsu, sai Barrister Jalo ya ce kadan ne daga cikin ‘yan siyasar Najeriya da ba “karuwan ‘yan siyasa ba.”
“Daga waccan jam’iyyar mutum ya yi kaura zuwa waccan jam’iyyar saboda mulki da kwadayi.” Inji Jalo
Har ila yau Barrister Jalo ya yi karin bayani kan makomar jam’iyyar inda ya ce tana bukatar addu’a.
“Makomar jam’iyyar PDP shi ne a taya mu addu’a, mu samu mu gane bakin zaren.”
Ga karin bayani a rahoton hirar Muryar Amurka da Barrister Abdullahi Jalo:
Your browser doesn’t support HTML5