Mai horar da ‘yan wasan Super Eagles na Najeriya Gernot Rohr ya ce tawagar ‘yan wasansa sun yi kewar Alex Iwobi da Wilfred Ndidi wadanda suke fama da jinya.
Rohr ya ambato ‘yan wasan ne bayan kaye da Najeriya ta sha a hannun Jamhuriyar Tsakiyar Afirka wacce ta lallasa Najeriya da ci 1-0 a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a 2022.
“Mun yi kewar kwarewar Alex Iwobi, sannan mun yi kewar Wilfred Ndidi sosai.” Rohr ya ce bayan an kammala wasan.
A cewarsa, Najeriya ce ta mallake wasan amma kuma ta gaza zura kwallo.
Dan wasan Jamhuriyar Tsakiyar Afirka Karl Namnganda ne ya zura kwallo a ragar Najeriya a minti na karshe a wasan wanda aka buga a ranar Alhamis a birnin Lagos da ke kudancin Najeriya.
Namnganda ya shiga wasan ne a matsayin dan canji wanda ya yi amfani da wata dama ya kutsa tsakanin masu tsaron gidan Najeriya ya doka kwallon ta wuce Francis Uzoho.
Duk da cewa a minti na 90 aka ci Najeriya, alkalin wasa ya kara minti takwas amma duk da haka ‘yan wasan na Super Eagles ba su kai labari ba.
Sai dai duk da wannan mamaya da suka sha a hannun ‘yan wasan na Jamhuriyar Afirka da ake wa lakabi da “Wild Beasts,” har yanzu Najeriya ce a saman teburin rukunin C inda take da maki 6.
Cape Verde da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka na da maki hudu-hudu, yayin da Liberia ke da maki uku.