Kungiyar duniya game da ‘yan gudun hijira ta duniya ta bada rahoton cewa, ana fa samun karuwar masu kokarin tarar aradu da ka don haurawa Turai daga kasashen yankunan Saharar Afirka.
Ta inda suke ratsawa ta cikin teku a manyan kwale-kwale da ke fuskantar hatsarin salwantar da rayuwarsu, bayan sun baro kan gabar tukun daga kasar Liya a kokarin tsallakewa zuwa Italiya.
Lisa Schlein ta kungiyar ‘yan gudun hijirar ta bayyana cewa, a ‘yan makonnin nan an ceci mutane da suka kusa halaka a cikin teku sama da 1000 zuwa wasu tashoshin jiragen ruwan Italiya.
Rahoton ya nuna cewa mafi yawancin mutuwar da ake yi tana faruwa ne sakamakon sikewar numfashi saboda karancin iskar da dandazon jama’ar da ke makare a jiragen ruwan za su shaka.