Har ya zuwa yanzu dai, masu zaben da suka kada kuri’unsu a jamhuriyar Nijar suna dakun jin nsakamakon zaben da aka aiwatar a makon da ya shude na shugaban kasa da ‘yan majalisu.
To sai dai kuma suna da sauran jiran da zai kai wata 1 nan gaba kafin a san wanda zai lashe zaben bayan zagaye na biyu da za a yin a zaben. Domin kuwa sakamakon da ya fito a ranar juma’ar shekaran jiya, ya nuna Shugaban kasar mai ci ya sami kaso 48 ne.
Wanda ya sa Muhammadu Issoufou din mai neman ta zarce a kan gaba. Shi kuma babban abokin adawarsa Hama Amadou yana manne da shi a baya a matsayin na biyu a zaben.
To amma kasancewa Issoufou bai kai kaso 50 daga jimillar kuri’un da aka kada ba yasa zai an yi zaben yada kanin wani. Tsohon Firaminista Hama Amadou dai yana garkame a gidan yari bisa zargin safarar jarirai.