Musamman ma daga fadawa hannun ‘yan kungiyar ta’addar ISIS da makamantansu?. Inji masu fashin baki. Taron zai yi tattaunawar musamman ne da zummar yadda za’a dakile yiwuwar barin makamashin Nukiliya daga fadawa hannun ‘yan ta’adda a duniya.
To sai dai mafasa bakin na ganin akwai gibi tsakanin Amurka da Rasha da su ne ke da muhimmiyar rawar takawa a taron.
Daraktan Tsare tsaren Gidauniyar Ploughshares Tom Collina, yace kashar Rasha na cikin jiga-jigan wannan taro, saboda haka ba karamin gibi bane idan ba su halarci taron ba wanda ya hada kasashe da dama, ciki har da Pakistan.
To amma dimbin bayanan da rasha ke da shi da ake bukatar musayarsu, ya kawo damuwar rashinta a wajen. Amurka da Rasha kadai suna da jimillar kamar kaso 90 na ingantaccen makamashin Nukiliya a duniya hade da jimillar fiye da rabin sinadaran makamashin Plutonium.
Collina ya ja hankalin cewa, mafi yawancin makamashin da ke kasashen da suka samu ta barauniyar hanya, an gano cewa daga Rasha suka fito.