Rashin Biyan Bashi Ga Mai Karamar Sana'a Babbar Illa Ce - Maryam Mu’azu

Maryam Mu’azu Muhammad, matashiyar ‘yar kasuwa ta koka ga yadda idan an karbin bashin kayanta yakan dauki lokaci fiye da yadda aka yi yarjejeniya tsakaninta da kwastoma wanda hakan ke kawo cikas ga yanayin kasuwanci.

Maryam, kamar kowacce mace me karamar sana’a ta ce sana’ar kaya mussamam ma dangogin mayafai da takalma da take sayarwa dole sai da bashi kasuwancin ke tafiya duk kuwa da ganin cewa kayayyakin da ake saye basu taka kara sun karya ba.

A mafi yawan lokuta akan bada kaya sai karshen wata a biya, idan an bayar a farkon wata a biya rabi amma wasu matan da zarar sun karba sai su fara wasan buya da masu kaya.

Ta ce rashin sana’a ga mace ba abu ne mai kyau ba sana’a wata hanya ce ta taimakawa kai, zama mai dogaro da kai sannan tana kashe kananan bukatu na ‘yan uwa maimakon yawan bani-bani daga wajen mai gida.

Your browser doesn’t support HTML5

Rashin Biyan Bashi Ga Mai Karamar Sana'a Babbar Illa Ce - Maryam Mu’azu