Maryam Abdulkadir – abin da na so na karanta a jami’a ba shi na samu na karanta ba domin kuwa Maryam ta so ta karanci harkar jarida sai aka bata kwas din special education maimakon Mass communication.
Ta ce ta fuskanci kalubale da dama domin a lokacinta idan aka basu aikin da zasu yi a gida wato assignment ba kamar yanzu bane da dalibi zai iya duba yanar gizo, suna zuwa dakin karatu ne wato library inda a mafi yawan lokuta basa samun abinda suka je nema sai a sami ko wani dalibin ya yage shafin littafi da makamantasu.
Sannan ta kara da cewa tana tsaka da karatun ne ta samu damar yin aure sai ga juna biyu , Maryam ta jaddada cewar kalubalen har sai da ta kai da kusan hakura da karatun, jajircewar maigidanta ya kara mata kaimi ta kamala.
Ko da yake bayan kamala karatun kalubalen da sauki domin akwai yanci ba kamar lokacin dalibta ba inji Maryam Abdulkadir.
Facebook Forum