Rashin Abinci A Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira Ya Fusata Majalisar Yaran Najeriya

Rabon abinci a sansanin yan gudun hijira

Majalisar yaran Najeriya mai suna Children Government Nigeria, ta baiwa gwamnatin tarayya kwanaki 30 da ta samar da abinci da kayayyakin more rayuwa ga yara da ‘yan gudun hijira dake sansanoni daban daban a fadin kasar.

Yaran wadanda suka fito daga jihohi 36 sun je jihar birnin Jos don mika korafinsu ga hukumar kare hakkin jama’a shiyyar Arewa ta tsakiya, kan halin kunci da ‘yan gudun hijira ke ciki a sassan daban daban na kasar.

A zantawar da wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji tayi da wasu yara ‘yan majalisar yaran Najeriya, sun bayyana mata cewa halin kunci da rashin abinci mai gina jiki da wasu sansanonin ‘yan gudun hijira a fadin Najeriya ke fama da shi, shine dalilinsu na baiwa gwamnatin kwana 30 don ta dauki mataki akai in kuma batayi ba to zasu kai ta zuwa kotu.

Majalisar ta kuma koka kan yadda ake cin zarafin yara ta hanyar yi musu fyade da fatauci da su, da ma yadda gwamnatoci da wasu mutane ke wawure kayayyakin agaji da wasu kasashe ke bayarwa suna barin ‘yan gudun hijiran da yunwa da takaici.

Jagoran yaran Patrick Ekpeme yace sun kirkiro majalisar yaran ne domin koyawa musu dabarun gudanar da mulki tun suna kanana.

Saurari cikakken rahotan Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

Rashin Abinci A Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira Ya Fusata Majalisar Yaran Najeriya - 3'30"