Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Oyo Zata Bayar Da Tukwici Ga Wanda Ya Bada Bayanin Kashe Dan Majalisarta


Yan sandan Najeriya a birnin Ibadan, jihar Oyo
Yan sandan Najeriya a birnin Ibadan, jihar Oyo

A kokarin da gwamnati keyi na gano wanda ya kashe dan Majalisar Dokokin jihar Oyo, mai wakiltar mazabar Orelope, Gideon Aremu.

Gwamnatin jihar Oyo, ta saka tukwicin Naira Miliyan Biyar ga duk wanda ya kwarmata mata ko su wanene suka kashe shi da kuma inda suke. Gwamnatin dai tace ta saka wannan kudi ne a bisa shawarar jami’an tsaro, da kuma zumudin ganin an damke duk wanda ke hannu kan wannan ta’asa.

Mista Yomi Layinka, kakakin gwamnatin jihar Oyo, “yace duk wanda yake da sahihin bayani game da wadanda suka kashe Gideyon Aremu, don aba jami’an tsaro bayani su kama su da hukuntasu gwamnatin jihar Oyo zata bada wannan makurken kudi Naira Miliyan Biyar.”

Yomi Layinka dai yace gwamnatin ta dauki wannan mataki ne na biyan tukwici ga duk wanda ya bayar da bayanai, don tabbatar da an yankewa wadanda suka aikata kisan hukunci. Idan mutum nada bayani sai a tuntubi gwamnatin jihar Oyo.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:31 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG