Rasha Ki Kwan Da Shiri, Harinmu Na Nan Tafe - Inji Trump

  • Ibrahim Garba

Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaba Trump ya mayarwa da Rasha martani dangane da alwashinta na kakkabo duk wani makami mai linzami da Amurka za ta harba akan Syria bayan harin makami mai guba da Amurka da kawayenta suka zargi Shugaba Bashar al- Assad da yin amfani da shi.

Bayan da Jakadan Rasha a Lebanon ya ce Rasha za ta kakkabo duk wani makami mai linzami da aka harba ma Syria, a yau Laraba Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Rasha ta kwan da shirin cewa harinmu, “na nan tafe.”

"Bai kamata ku yi abota da dabba mai kashe mutane yana jin dadi ba,” Trump ya rubuta a shafinsa na Twitter.

​Rasha ta mayar da martani da cewa kamata ya yi makami mai linzamin Amurka ya auna ‘yan ta’adda, amma ba a kan, “halattacciyar gwamnatin Syria ba.”

A halin yanzu dai Syria na cikin fargaba, tun wani harin da ake zargi na makami mai guba ne a ranar Asabar a gabashin Ghouta, inda ya kashe akalla mutane 40.

Kasar Amurka da abokan huldarta da dama sun raja’a ga cewa sojojin Syria ne su ka kai harin, yayin da Syria da Rasha kuma suka karyata zargin cewa sojojin Shugaba Bashar al-Assad ne ke da alhakin harin.