Kasar Rasha ta ce tuhumar da Amurka ta yi ma wasu ‘yan Rashar 13 da wasu kamfanonin Rasha uku bisa zargin cewa sun yi katsalandan a zaben Amurka na 2016 sokiburutsu ne kawai.
Da ya ke magana a wurin wani taro kan batun tsaro a Munich na kasar Jamus, inda dinbin Shugabannin kasashen duniya su ka taru a karshen wannan satin, Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov ya jefa ayar tambaya kan sahihancin hujjojin da Ma’aikatar Shari’ar Amurka da kuma mai bincike na musamman Robert Mueller, su ka gabatar.
“Kun san ni ban da abin fadi ko muskalazaratin, saboda mutum na iya wallafa duk abin da ya ga dama. Ai mun ga yadda zargi, da kalamai da kazafi ke yado. Muddun ba mu ga shaida ba, duk wani abin da ake cewa shirme ne kawai. Don Allah a mani azuri saboda rashin amfani da lafazi irin na diflomasiyya.” In ji Lavrov.