Rasha Ta Sha Suka Akan Kasar Ukraine

Masu goyon bayan Rasha dake da makamai cikin kasar Ukraine

Masu goyon bayan Rasha dake da makamai cikin kasar Ukraine

A wani taron gaggawa da kwamitin sulhu na Maljalisar Dinkin Duniya yayi Rasha ta sha kakkausar suka akan kasar Ukraine
Rasha ta sha kakkausar suka daga manyan kasashen duniya a lokacinda kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yayi wani taron gaggawa jiya lahadi kan rikicinda ake yi a Ukraine, a dai dai lokacinda mummunar arangama ta barke tsakanin magoya bayan Rasha ‘yan aware, da kuma magoya bayan gwamnatin kasar a gabashin Ukraine din.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Samantha Powers, da jakadan Ingila Mark Lyall Grant sun zargi Rasha da zama kanwa uwar gamin tarzomar da ta barke.

Jakadiyar ta Amurka tace “baki daya rikicinda yake aukuwa a Ukraine mutum ne ya kitsa shi, tace an shirya fitinar ce baki daya daga Rasha inda daga canne ake samun umarni kan yadda za’a tafiyar da ita.

Shi kuma jakadan na Ingila yayi kira ne ga kwamitin sulhun ya ja kunnen Rasha ta guji daukan karin wasu matakin soji a Ukraine.

Rasha wacce itace ta kira taron kwamitin sulhun taki ta amince da wannan zargi. Maimakon haka, jakadantaa a Majalisar Dinkin Duniya, Vitaly Churkin, yayi kira ga kwamitin sulhun ya kira hukumomin Ukraine su daina amfani da karfi kan mutanen da suke gabashin Ukraine, wadanda galibinsu masu magana ne da harshen Rasha.

Taron a Majalisar Dinkin Duniya yazo ne gabannin karewar wa’adin da Ukraine ta baiwa mayakan sakai masu goyon bayan Rasha su ajiye makamansu.