A yau Juma’a, kasar Ukraine ta bayyana cewar ta karbi gawawwaki 563 daga hukumomin Rasha, galibinsu sojoji ne da aka kashe a yaki a gabashin yankin Donetsk.
Musayar fursunoni da gawawwakin sojojin da aka kashe ce ta kasance hanya daya tilo ta yin hadin gwiwa tsakanin hukumomin Moscow da Kyiv tun bayan mamayar Rasha a 2022.
“An maidowa da Ukraine da gawawwakin dakarunta 563 da suka mutu a fagen daga,” a cewar sanarwar da shelkwatar kula da fursunonin yaki ta wallafa a shafinta na sada zumunta.
Sanarwar na wakiltar aikin dawo da gawawwakin sojojin Ukraine da aka hallaka a filin daga mafi girma tun bayan barkewar yakin.
A cewar sanarwar, an dawo da 320 daga cikin gawawwakin ne daga yankin Donetsk da kuma sojoji 89 da aka hallaka kusa da garin Bakhmut, wanda Rasha ta kwace a watan Mayun bara bayan mummunar daga.
Har ila yau, an dawo da karin gawawwaki 154 daga dakunan ajiyar gawa dake Rasha, a cewar sanarwar.
Babu daya daga cikin Rasha da Ukraine daya taba bayyana yawan dakarunsa da aka hallaka a fagen daga.