Rasha Ta Kai Hari Kan Muhimman Ababen More Rayuwa A Yammacin Ukraine - Rundunar Sojin Sama

Harin da Rasha ta kai kan muhimman ababen more rayuwa a yammacin Ukraine

Harin ya sabbaba daukewar lantarki a wani sashe na birnin Ternopil, a cewar magajin garin yankin, mako guda bayan da hare-haren Moscow suka katse lantarki ga galibin birnin da kewayensa.

Harin ya sabbaba daukewar lantarki a wani sashe na birnin Ternopil, a cewar magajin garin yankin, mako guda bayan da hare-haren Moscow suka katse lantarki ga galibin birnin da kewayensa.

Masu kashe wuta a Ukraine bayan harin da Rasha ta kai

“Ma’aikatan lantarki da na ceto na kokarin kawar da illolin harin. Ku tara ruwa, tare da caza wayoyinku,” kamar yadda magajin gari Serhiy Nadal ya bayyana a sakon daya aike ta shafinsa na Telegram.

Birnin Ternopil na da tazarar kimanin kilomita 220 daga gabashin kasar Poland wacce mamba ce a rundunar tsaro ta NATO.

A watan Nuwambar da ya gabata Rasha ta kaddamar da manyan hare-hare guda 2 akan tashoshin lantarkin Ukraine, abinda ya sabbaba katsewar lantarki a fadin kasar a shirye-shiryen tunkarar hunturu.

Rundunar sojn saman Ukraine ta ce ta kakkabo 22 daga cikin jirage marasa matuka 28 da Rasha ta harba mata a daren jiya. Jirgi maras matuki guda daya ya “bata” sannan 2 sun fice daga sararin samaniyar Ukraine, a cewar sanarwar.

Har ila yau Rasha ta kaiwa tashar lantarki dake yankin Rivne, a cewar gwamna Oleksandr Koval, ya kara da cewar, babu wanda hare-haren suka hallaka.

An tsananta tsaron sararin samaniya a yankin Kyiv cikin dare, a cewar Gwamna Ruslan Kravchenko. baraguzan gine-gine sun lalata gidajen zama 4 da motoci 2 da wani gareji, a cewarsa.

-Reuters