Rasha Ta Zargi Amurka Da Kwadayin Mulkin Mallaka

Kasar Rasha ta fada yau talata cewa, sabuwar manufar tsaron kasa da Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana ba komai bace illa kwadayin mulkin mallaka, wadda kuma ta nuna Amurka bata amince da ra'ayi ko akidar kowa ba sai tata.

Kakakin fadar shugaban Rasha ta Kremlin, Dimitri Peskov, yace Rasha bata amince da kallon da Amurka take yi mata a matsayin mai barazanar tsaro ba, amma tana maraba da yunkurin gwamnatin Trump na yin aiki tare akan muradun da suka shafi kasashen biyu.

A jiya Litinin Shugaba Trump ya bayyana sabuwar manufar tsaron kasa, inda yake gargadin cewa, akwai wasu kasashen da ke kalubalantar karfin Amurka, yana mai lasar takobin cewa Amurka zata yi amfani da duk abinda take da shi wajen farfadowa da kuma nuna karfin a duniya.

Manufar ta tanadi Amurka zata hada kai da masu adawa da karfinta ko gasa da ita, musamman ta hanyar tabbatar da cewa karfin sojan Amurka yafi na kowace kasa a duniya, wadda kuma zata hada kai da dukkan kawayenta.

Trump ya bayyana Rasha da Chana a matsayin manyan damuwarsa, yace kasashen biyu suna kalubalantar darajar Amurka da tsarinta da arzikinta da kuma karfinta.