Bankin bada lamuni na duniya sun bayyana cewa, Najeriya ta sami sassaucin fatara sakamakon kyawun amfanin gona da aka samu a bana, maimakon yawan dogara da man fetur kacokan da kasar ke yi duk da halin hawa da saukar farashin man fetur a duniya.
Musamman idan aka yi la’akari da yadda sabon hasashen kasafin kudin na badi zai maida hankali akan samun kudaden shiga daga harajin da ke bullowa daga hukumar hana fasa kwauri da makamantansu, maimakon kwallafa rai akan gangunan man fetur din da ake .hakowa a kasar.
Sai dai masana na ci gaba da tsokacin kan lamarin na yadda suke auna shekarar 2017 da ke bankwana tare da hango shekarar 2018 da ke tafe. Shahararren dan kasuwa Umar Mutallab ya bayyana yadda suke kokarin hada fahimtar da al’ummar Nijar yadda za su fahimci hadakar kiyaye kan iyakoki da inganta shige da fice don amfanar juna.
Daya daga cikin kwamishinonin kudi a Najeriya Hassan Muhammad ya bayyana cewa, rufe kan iyakokin kasa ma ba alheri bane. Ya kara da cewa abinda kawai ake bukata shine hukumar Kwastam su yi aikinsu yadda ya dace.
Muhammad Bashir Kiri kuwa mai tsokacin al’amura ne, kuma magana yayi da yawun talakawa na yadda ake cewa an fice daga fatarar da aka fada a Najeriya, tare da kawo misalin yadda har yanzu wasu ba sa iya cin abinci sau uku a rana a kasar, amma ana ta maganar an fice daga fatara.
Facebook Forum