A yau Talata, Majalisar Dokokin Rasha ta amince da kudirin da zai iya share hanyar da Moscow za ta tsame Taliban daga jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda.
Mahukuntan birnin Moscow sun jima suna zawarcin kungiyar Taliban bayan da ta karbe ragamar mulkin Afghanistan sakamakon janyewar da Amurka ta yi cikin rudani a 2021.
Tun sa’ilin jami’ai ke kokarin cire sunan kungiyar mai ra’ayin Musulunci daga jerin kungiyoyin ‘yan ta’addar da Moscow ta haramta.
Majalisar Dokikin Rasha, Duma, ta zartar da kudirin da ya fayyace hanyoyin da za a bi wajen tsame kungiyar daga jerin sunayen ‘yan ta’adda, inda aka fitar da dukkanin dokokin da ake bukata domin tsaida matsaya a nan gaba.
Majalisar Dattawan Rasha za ta yi nazari a kan kudirin Juma’a mai zuwa, gabanin mika shi ga Shugaba Vladimir Putin domin zartar da shi a matsayin doka.