Rasha Da China Na Sake Fasalin Kawance Da Dangantaka Da Iko A Duniya - Tidd

Admiral Kurt Tidd, babban kwamnadan rundunar sojin ruwan Amurka na kudancin nahiyar Amurka

Rasha da China na samun nasara wurin sake fasalin kawance da dangantaka da iko a duk fadin duniya abun da kuma shugabannin Amurka basu maida hankali a kai ba a cewar Admiral Kurt Tidd

Rasha da China suna samun nasara wajen sake fasalin kawance dangnataka da iko a fadin duniya, lamarti dake damun Amurka da kawayenta.

Kodashike manyan jami'an soja sun sha jan hankali kan take taken Rasha da China a wasu sassan duniya, daga Turai zuwa yankin Asiya, da Afirka, akwai alamun cewa Amurka da kawayenta basa kula ko maida hankali nan kusa da gida kan take taken kasashen biyu a kudanci da kuma kasashe dake nahiyar Amurka ta tsakiya.

Kwamandan mayakan ruwa na Amurka Admiral Kurt Tidd mai kula da shiyya kudu yace, a nan kusa da gida akwai gasa mai tsanani dake wakana.

Rahotanni suka ce Rasha tana kara matsa kaimi wajen sake dawo da martabarta ta fuskar soja, ta wajen aikewa da jiragen yakinta na ruwa zuwa yankin tare da kara tattara bayanann sirri.

Baya ga kara farfado da dangantaka da tsoffin kawayenta, kasar ta dukufa wajen sayar wa kasashen kayan yaki. Daya daga cikin kasashen da suka amfana karkashin yunkurin ita ce Venezuela.