Amurka ta ce da China da Rasha masu yada tashin hankali a duniya ne, saboda yadda su ke kin kiyaye hakkin dan adam; haka ma Koriya Ta Arewa da Iran.
WASHINGTON D.C. —
A rahotonta na shekara-shekara kan hakkin dan adam wanda ta fitar jiya Jumma’a, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta zargi kasashen hudu da take hakkin dan adam, ciki har da batun ‘yancin fadin albarkacin baki da batun kare tsirarun mabiya wasu addinai da kuma kananan kabilu.
Mukaddashin Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Sullivan ya fadi a babin gabatarwa na rahoton cewa kasashen hudu “su na take hakkin mutanen da ke cikin kasashensu kulluyaumin.”