Rarrabuwar Kawuna Tsakanin Mahukuntan Najeriya

Majalisar Dattawan Najeriya

Yayin da dangantaka ke kara tsami a tsakanin bangaren majalisar dokoki da ta zartarwa, manazarta da kuma lauyoyi na ganin akwai bukatar karatun ta natsu a tsakanin bangarorin biyu kamar yadda yake a bisa tsarin demokaradiyya.

To sai dai yayin da lamarin ke tafiya dai dai a wasu kasashe da alamu a Najeriya dake zama babbar yaya ta Afrika, zaman ‘yan marina ake yi musamman a tsakanin bangaren ‘yan majalisa da kuma fadar shugaban kasa.

Na baya bayan nan ma shine satoka-sa-katsin dake faruwa yanzu a tsakanin mukaddashin shugaban kasa Yemi Osibanjo da kuma yan majalisar dattawa, inda yan majalisar ke neman mukaddashin shugaban kasan da ya janye kalaman da yayi game da batun mukamin shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu.

To sai dai yayin da ake ci gaba da cece-kucen manazarta da kuma wasu ‘yan Najeriya na ganin akwai bukatar karatun ta-natsu a tsakanin bangarorin biyu, musamman a wannan lokaci da kasar ke mawuyacin hali na batun sake duba makomar kasa daya al’umma daya.

To ko yaya yan Najeriya ma ke kallon wannan danbarwa a yanzu? Abdullahi Bazza, wani dan Najeriya dake ganin akwai bukatar a duba lamarin.

Adamu Modibbo wani dan siyasa kuma masanin shari’a a Najeriya, ya ce shi bai ga wani abin tada jijiyar wuya ba, tunda akwai mafita a yanzu.

Kawo yanzu dai Ibrahim Magu na ci gaba da rike mukamin shugabancin hukumar ta EFCC, wanda kuma lokaci ne ke iya tabbatar da yadda zata kaya, shin za’a je kotun ne ko kuma a’a?

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Rarrabuwar Kawuna Tsakanin Mahukuntan Najeriya - 4'17"