Jami’an tsaron Yemen da magoya bayan shugaban wata kabila sun kara a wajajen fitar birnin Sana’a, fadar kasar.
Shaidu suka ce daruruwan magoya bayan Sheikh Sadeq al-Ahmar, suna kokarin kaiwa ga unguwar Hasaba dake Sana’a, inda shugaban yake da zama, tuni dakarun gwamnati suke fatattakar unguwar. Sunce an kashe mutane da dama a fadan da ake yi.
Lamarin yasa an tsaida zirga zirgan jiragen sama a tashar jirage a Sana’a babban birnin kasar, sakamakon zafafa fada tsakanin dakarun gwamnati da kabilun,kuma fadan ya kai kusa da tashar.
Sojojin gwamnati sun bude wuta kan masu zanga zangar neman kawo Karshen mulkin shugaba Ali Abdullah Sale. ‘Yan gwagwarmaya sunce an kashe akalla mutane ashirin da biyar a fadace fadace da ake yi a yankin cikin ‘yan kwanaki da suka wuce.
Rikicin na Yemen ya sa wasu kasashe rage yawan jami’an jakadancinsu a kasar,ko kuma su rufe ofisoshinsu baki daya.