Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta bada rahoton cewa ci gaba da rikici da yaki da ake yi a Somaliya, hakan na kara yawan kananan yaran dake kamuwa da cututtukan dake kaisu ga mutuwa.
Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, a sabon rahoton da ta bayar hantsin Alhamis na cewa yaran da shekarunsu na haihuwa ke kasa da biyar ne suka fi cutuwa daga harbe-harben bindigogin dake zubda harsasai masu guba musamman a Mogadishu, baban birnin kasar Somaliya.
Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya tace manyan dalilan dake janyo mutuwar yaran sun hada da konewa da ciwon kirji da kuma matsalar zubda jini bayan shaker hayakin harsasan da ake harbawa.
Sojin hadin gwiwar kungiyar Tarayyar Afirka da Gwamnatin Somaliya na ci gaba da kai hare-haren kauda barazanar mayakan ‘yan tsagerar al-Shabab dake Somaliya da suka ja daga a ciki da kewayen Mogadishu. Al-Shabab, ta lashi takobin ganin ta hambaras da Gwamnatin Somaliya da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya domin maye gurbinta da Gwamnatin Islama.
Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO tace tace ta kammala horas da likitoci sama da hamsin da kuma ma’aikatan jiyya da yanzu ke aiki a babban Asibitin Banadir a birnin Mogadishu da niyyar tababtar da baiwa kanannan yara kulawar da ta dace.