Ranar biyu ga watan Nuwamba rana ce ta musamman da Majalissar Dinkin Duniya ta ware don yin nazari aka yadda ake kuntatawa ‘yan jarida.
WASHINGTON DC —
Farfesa Bello Bada, na jami’ar Usman Danfodiyo dake Sokoto ya ce, aikin jarida na daya daga cikin muhimman ayyukan da suka wayar da kan mutane a nahiyar Afrika matuka, musamman gameda harkokin gwamnati.
Sai dai duk da irin kokarin da ‘yan jaridar ke yi suna fuskantar kalubale a fadin duniya, ba kamar ma a kasashen Afrika. Farfesa Bada yace a kasashen Afrika ba a cika mutunta hakkokin 'yan jarida ba kuma yawancin shugabannin kasashen nahiyar sun saba da mulkin mallaka, ba sa so a kalubalance su.
Ya cigaba da cewa akan kuntatawa ‘yan jarida da ‘yan uwansu, wasu kuma akan tilas su ke gudun hijira. Farfesa ya ja hankalin jama’a akan su fito su ba ‘yan jarida goyon baya domin suna aiki ne a madadin su.
Your browser doesn’t support HTML5