Hon. Hussaini Gambo Bello, daya daga cikin manyan manoman shinkafa a jihar Adamawa, ya koka game da yadda kawo yanzu manoma a jihar basu soma cin gajiyar shirin baiwa manoma rance da gwamnatin tarayya ta kaddamar ba, wanda ake wa lakabi da “Anchor Borrowers.”
An dai yi zargin cewa da gangan bankin manoma ya ki baiwa manoma kudaden da Babban Bankin Najeriya, CBN, ya fitar domin baiwa manoma a karkashin shirin na gwamnatin tarayya a jihar Adamawa .
To sai dai kuma shugabar gudanarwar bankin shiyar Yola, Madam Mary Buba ta fada a wajen taron masu ruwa da tsaki kan harkokin noma da tallafawa manoma a jihar, cewa ita tuni ta tura shelikwatar bankin, to amma kawo yanzu bata san ko an rattaba hannu akai ba ko a’a.
‘’Mu mun kammala tura sunayen manoman daga wannan shiya zuwa shedikwatar mu, kuma na samu labarin an tura sunayen zuwa teburin MD, to amma ban san ko an sa hannu ko kuma a’a ba, amma ina da yakinin cewa za’a kammala, don an soma biya,’’ a cewar ta.
To ko anya taron zai kai ga share hawayen manoma a jihar? Dr Umar Bindir, sakataren gwamnatin jihar da ya jagoranci taron, ya bada tabbacin cewa zasu yi zare dantse don ganin manoma sun ci gajiyar shirin a jihar.
Mallam Ahmad Umar Waziri wanda shi ne manajan Babban Bankin Najeriya, CBN a jihar, yace yanzu kam sun gano bakin zaren.
Kimanin Naira biliyan 44 ne dai Babban Bankin Najeriya CBN ya fitar domin tallafawa manoma inda kawo yanzu kusan jihohi 29 suka soma cin gajiyar shirin, amma babu jihar Adamawa a cikin jerin jihohin da shugaba Buhari ya lissafa ya kuma yaba ma Gwamnoninsu a kokarin da suka yi kan harkar noma, batun da wasu ke ganin akwai abun dubawa.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Facebook Forum