Ranar Yaki Da Cutar Shan Inna

Ranar yaki don kawar da  cutar shan inna a duniya.

Hukumar lafiya ta duniya ta ware ranar 24 ga watan Oktoba na kowacce shekara a matsayin ranar yaki don kawar da cutar shan inna a duniya.

Taken ranar na wannan shekarar shine ‘samar da ingantacciyar lafiya ga iyaye mata da kananan yara’.

Najeriya na daya daga cikin kasashen Africa da aka tabbatar da sun yi nasara wajen kawar da cutar shan inna.

Ranar yaki don kawar da cutar shan inna a duniya.

Hakan ya fito ne daga bakin Daraktan tsare-tsare, bincike da kididdiga na humar lafiya matakin farko ta Najeriya Dr. Abdullahi Bulama Garba.

A hirar shi da Muryar Amurka Dr. Bulama yace kalubalen da suke fuskanta a yanzu shine akwai cuta mai kama da cutar shan inna da kananan yara su ke kamuwa da ita sakamakon rauni na garkuwar jiki ga yaran da basu samu cikakken rigakafi ba, inda ya kara da cewa suna aiki tukuru don ganin an shawo kan wannan.

Daraktan ya kara da cewa sun samu nasarar kawo karshen cutar shan inna na dindindin ne da hadin kai malamai, shugabannin gargajiya da kuma al’umma, yana mai cewa duk da wannan nasarar zasu cigaba da aiki don ganin cewa ba’a kara samun bullar cutar ba a Najeriya.

Dr. Bulama Garba ya jaddada muhimmancin rigakafi a matsayin babban makami dake kare yaduwa da kuma aukuwar cututtuka a tsakanin al’umma.

Bincike ya nuna cewa akwai sauran kasashe biyu da basu kawar da cutar ba da kuma wata kasa a yammacin turai.

Saurari rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Ranar Yaki Da Don Kawar Da Cutar Shan Inna