Ranar Ma'aikata Ta Duniya: Kungiyoyi Da Gwamnatin Nijar Zasu Tattauna Akan Inganta Yanayin Aiki A Kasar

Ranar Ma'aikata Ta Duniya A Nijar

Kungiyoyin kwadago sun bayyana irin bukatunsu da sukace suna fafutukar ganin gwamnati na samar musu da wata mafita wanda zai dace da halin matsin da ake ciki a yanzu a Nijar.

Daya ga watan mayu rana ce da aka ware a duk shekara a matsayin Ranar Ma’aikata ta Duniya domin yin waiwaye adon tafiya akan nasarori da ma’aikata suka samu da kuma matsalolin ko kalubalen da suka fuskanta a kasashe daban daban.

Ranar Ma'aikata Ta DUniya A Nijar

Saidai ranar tazo wa ma’aikatan Nijar daidai lokacin da kasar ke fama da hauhawar farashin kayan masarufi, lamarin da yassa ma’aikatan kokawa kan yadda albashi baya iya biya musu bukatu na yau da kullum.

Kungiyoyin Ma’aikatan sun bukaci gwamnatin Nijar da ta kawo karshen kwantiragi domin inganta harkokin aiki a kasar.

Ranar Ma'aikata Ta Duniya A Nijar

Ma’aikatan a karkashin kungiyoyin su sun fito inda suka gudanar da jerin gwano a gaban gwamnonin jihohi kamar yadda aka saba a kowace shekara domin mika kokensu.

Ranar Ma'aikata Ta DUniya A Nijar

Hukumomi sun karbi koken ma’aikatan tareda bayyana musu cewa zasu zauna kan teburin tattaunawa.

A saurai cikakken rahoton Hamid Mahmud:

Your browser doesn’t support HTML5

Ranar Ma'aikata Ta Duniya: Kungiyoyi Da Gwamnatin Nijar Zasu Tattauna Kan Inganta Harkokin Aiki A Kasar