Ranar Fadakarwa Kan Cutar HIV/AIDS

Ranar Fadakarwa Kan Cutar HIV ta Duniya

Yau ne a fadin duniya ake gudanar da gangamin wayar da kan Jama’a game da batutuwan da suka shafi cuta mar karya garkuwan Jikin bil’adama wato HIV/AIDS.

An dai fara wannan gangami ne tun a shekara ta 1988 aka fara gangamin wayar da kan al’umma game da cutar HIV, bayan da MDD ta ware ranar daya ga watan Disambar kowacce shekara domin fadakar da mutane game da wannan cuta.

Gangamin shekara shekarar dai kari ne akan wanda ake yi a Asibitoci da cibiyoyin bada magani ga masu dauke da larura a sassan Duniya.

Wakilin Muryar Amurka a jihar Kano, Mahmud Ibrahim Kwari, ya ziyarci Asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano, inda malaman kiwon lafiya ke fadakarwa ga masu dauke da cutar. A zantawarsu da Fatima Mohammad wata mai dauke da cutar, wadda tace yanzu haka tana samun lafiya sosai kuma bata boye kanta a matsayin wadda ke da HIV, tare da zaman lafiya da kowa.

Shi kuma Muktar Wada Zakari Yakasai, yace a kamu da cutar ne a shekara ta 2004 ya kuma kwashe shekaru uku yana shan wahala, amma yanzu ya samu sauki sosai da sosai.

Shugabar cibiyar kula da masu larurar HIV a Asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano, Salamatu Mu’azu, tace fadakarwar yau da kullum da fadakarwa ta kafafen yada labarai na tasiri matuka, saboda yana taimakawa mutane su fahimci muhimmancin shan magani da kwantar da hankali.

Najeriya dai na daga cikin jeri kasashen duniya da al’ummarta ke fama da cutar HIV, inda fiye da mutane Miliyan shida ke dauke da cutar a cewar shugaban kula da hukumar yaki da cutar HIV/AID ta jihar Kano. Haka kuma yace mutane Miliyan uku ne ke kan magani.

Rahotannin dai na nuni da cewa masana kiwon lafiya a kasar Afirka ta Kudu sun gano sinadarin wannan cuta ta HIV/AIDS.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ranar Fadakarwa Kan Cutar HIV/AIDS - 3'31"