Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alfanun Yin Anfani da Tasoshin Jiragen Ruwa Na Kan Tudu


 Babban Darakta Barrister Ahmed Rabiu na hukumar harkokin jiragen ruwan Najeriya
Babban Darakta Barrister Ahmed Rabiu na hukumar harkokin jiragen ruwan Najeriya

Yunkurin magance wahalar da ake sha wajen tantance kayan da ake shigo dasu ta tasoshin jiragen ruwan Najeriya ya sa hukumar harkokin jiragen ruwan Najeriya ko Nigerian Shippers' Council kara kaimi wajen fadakar da 'yan Najeriya akan alfanun dake akwai wajen fara yin anfani da tasoshin jiragen ruwa na kan tudu ko Inland Dry Port a turance

Yayinda yake jawabi a wurin wani taro da hukumar kula da harkokin jiragen ruwan Najeriya ta gudanar a garin Kaduna daya daga cikin daraktocin hukumar Mr. Ignacious Nweke da ya wakilci babban daraktan hukumar na kasa yace duk irin hada hadar da aka saba gani a tasoshin jiragen ruwan dake Legas su ne za'a dinga gani a tasoshin na kan tudu dake arewacin kasar.

Malam Muhammad Gazali Abdulsalam shugaban kungiyar masu harkokin jiragen ruwa ta Najeriya shiyar jihar Kaduna ya halarci taron.Yace dalilin kiran taron shi ne waye kan jama'a su san cewa yanzu ba sai an je Legas ba. Idan ana son a kawo kaya daga kasashen waje ko a aika da kaya kasashen waje ba sai an je Legas ba. Duk abun da za'a yi a tashar Legas ana iya yinsa a tashar Kaduna.

Yanzu dai kamfanonin sufuri ne zasu dinga kawo kayan amma ana fatan gwamnatin tarayya zata taimaka da hanzarta fadada ayyukan layin dogo wanda zai yi tasiri a ayyukan tashar.

Ayyukan tasoshin zasu bunkasa tattalin arzikin arewa saboda tasoshin zasu kawo ayyukan yi daban daban.Matasa zasu samu aikin yi. Gwmnati ma zata karu da kudaden haraji.

Ga rahoton Isa Lawa Ikara da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:02 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG