Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Darajar Naira A Najeriya Zata Ci Gaba Da Faduwa


Takardun Kudin Kasar Najeriya
Takardun Kudin Kasar Najeriya

Bincike ya nuna cewa darajar Naira zata ci gaba da faduwa yayin da kuma daga watan Disamba zuwa farkon shekara mai zuwa za a sami karin farashin kayayyakin masarufi a Najeriya.

Babban bankin Najeriya ne ya gudanar da wannan binciken, inda ya gano cewar matsalar wutar lantarki itace babbar damuwa ga hada hadar tattalin arziki a Najeriya. sauran matsalolin sun hada da matsalar kudi da yawan kudin ruwa da rashin kyakkyawan yanayin hada hadar kasuwanci da kuma rashin kyakkyawan dokokin tattalin arziki.

Sai dai wani masani kuma mai sharshi kan al’amuran yau da kullum Baba Yola Mohammdu Tanko, na ganin wannan ra’ayin babban bankin Najeriya ne kawai, domin idan gwamnati kara matse shigowa da kayayyaki daga kasashen waje da ci gaba da yin amfani kayan da ake dasu a cikin gida, wanda hakan zai dakile tashin Dalar.

Shi kuma masanin tattalin arziki Yusha’u Aliyu, na ganin idan har gwamnati zata shigo da abincin da zai taimakawa kasuwa da dai dai ta farashi ta yadda mutane zasu iya saya. Domin duk wannan matsala ta farune domin wasu ‘yan kasuwa na boye abinci da kuma kulle kasuwa da akayi wanda tattalin arzikin kasar ya dogara a kanta.

Saurari cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG