Ranar Da Ronaldo Zai Fara Buga Wasa A Saudiyya

Ronaldo

Ronaldo na fuskantar jinkiri wajen fara bugawa Al-Nassr wasa ne saboda yana karkashin wani hukunci na dakatar da shi da aka yi daga buga wasa na wani lokaci, saboda ya buge waya a hannun wani dan kallo a watan Afrilu a lokacin yana United.

Tun bayan da ya koma kungiyar Al-Nassr ta kasar Saudiyya, masoyan Cristiano Ronaldo suke ta shaukin ganin ranar da zai fara wasansa na farko a kungiyar.

Ronaldo da Manchester United sun raba gari a watan Nuwamba, bayan rashin jituwa da aka samu tsakaninsa da jagororin kungiyar.

Akwai rahotanni da ke cewa akwai yiwuwar wasan da zai fara bugawa zai zamanto karan-batta tsakaninsa da Lionel Messi na kungiyar PSG.

Wasu za su yi mamaki me ya hada gasar Saudiyya da kungiyar PSG.

Abin da ke faruwa shi ne, an shirya wani wasan sada zumunta tsakanin gamayyar ‘yan wasan Al-Nassr da Al-Hilal na Saudiyya da kuma kungiyar PSG.

Ana kuma hasashen akwai yiwuwar Ronaldo zai buga wasan amma ba sanye da rigar Al-Nassr ba.

Za a buga wasan ne a birnin Riyadh a ranar 19 ga watan Janairu, kamar yadda mai horar da ‘yan wasan Al-Nassr Rudi Garcia ya fada a wata hira da ya yi da jaridar wasanni ta Le’Equipe.

Ronaldo na fuskantar jinkiri wajen fara bugawa Al-Nassr wasa ne saboda yana karkashin wani hukunci na dakatar da shi da aka yi daga buga wasa na wani lokaci, saboda ya buge waya a hannun wani dan kallo a watan Afrilu a lokacin yana United.

Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa, Ronaldo mai shekaru 37, zai fara buga wasa a ranar 22 ga watan Janairu inda Al-Nassr za ta fafata da Ettifaq