Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta ware duk ranar 12 ga watan Agusta a matsayin ranar matasa, don duba ga matsaloli da kuma hanyoyin warware su a fadin Duniya.
Wakilin Muryar Amurka ya zagaya birnin Ibadan, inda ya zanta da matasa domin jin wane irin matsaloli suke fuskanta. Yawancin matasan da suka yi magana sun nuna rashin jin dadinsu ga rashin kulawar da ake musu.
Babbar matsalar da ke damun matasan dai ba ta wuce rashin samun aiyukan yi ba, wanda suke nemi shugabanni da su tashi tsaye wajen samar da ayyukan yi da zasu basu damar samun rayuwa mai inganci.
A wannan zamani dai wasu ‘yan siyasa na amfani da matasan wajen basu kudi da tsunduma su cikin bangar siyasa.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Umaru Tambuwal.
Your browser doesn’t support HTML5